Ta'addanciNajeriya
Najeriya: Gumurzun 'yan bindiga da sojoji
July 24, 2025Talla
Wannan na kunshe ne cikin wani rahoto na halin da ake ciki da aka bai wa Majalisar Dinkin Duniya, wanda kuma kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ce ya gani. Rahoton ya nunar da cewa, lamarin ya afku ne a farkon wannan makon da muke ciki yayin arangama tsakanin sojojin da 'yan bindigar da suka addabi yankunan Najeriyar da dama. Lamarin rashin tsaro na kara ta'azzara a Najeriyar, kasar da ke fama da matsalar talauci da rashin ci-gaban yankunan karkara da kuma halin ko-in-kula daga gwamnati.