Rikice-rikiceNa duniya
Ta ya za daina take dokokin kasa da kasa?
September 8, 2025Talla
Volker Turk ya bayyana hakan ne, yayin da yake jawabi a taron Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniyar karo na 60. Ya yi gargadin cewa, abubuwan damuwa da ke da tayar da hankali na samun wajen zama a duniya. Ya nunar da yadda aka yi fatali da dokokin kasa da kasa a yakin Rasha da Ukraine da yakin basasar da ake fama da shi a Sudan da kuma na Isra'ila da Hamas, wanda ke ci gaba da tarwatsa al'ummar yankin Zirin Gaza na Falasdinu. Jawabin nasa na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da Chaina ta gudanar da wani gagarumin faretin soja da baje-kolin sababbin makamai na zamani, yayin da a hannu guda shugaban Amurka Donald Trump ya canza sunan ma'aikatar tsaron kasar zuwa ma'aikatar yaki.