SiyasaTurai
Akwai sulhu tsakanin EU da Amurka a kasuwanci?
May 30, 2025Talla
Shugaban kwamitin kasuwanci na majalisar Tarayyar Turan Bernd Lange ne ya bayyana hakan, yayin wata hira da ya yi da gidan radiyon Deutschlandfunk na Jamus. A cewarsa ba za su yadda a cimma yarjejeniyar da Amurkan za ta sake bijiro da sabon haraji kwanaki kalilan bayan amincewa da ita ba, yana mai cewa da zarar hakan ta kasance Tarayyar Turai ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen mayar damartani da irin nata harajin.