Amnesty: M23 na cin-zarafin mata a Kivu
August 21, 2025Rahoton ya ce wadannan laifuka na iya zama laifukan yaki, a karkashin dokokin kasa da kasa. Wannan aikin bincike da kungiyar Amnesty International ta gudanar, ta yi ne bayan tattaunawa da mutane fiye 53 ciki har da matan da aka ci-zarafinsu a arewaci da kudancin Kivu. Rahoton na kungiyar ta Amnesty International ya nuna cewa dakarun M23 da Wazalendo, dukkansu sun aikata cin zarafi ga fararen hula. Kimanin mata 14 aka yi wa fyade, inda takwas daga cikinsu ke zargin dakarun M23 biyar kuma na zargin Wazalendo yayin da daya ta ce sojojin gwamnati ne suka yi mata hakan.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta ce, an kashe mutane fiye da 140 a yankin Kivu ta Arewa a watan Yuli kadai kuma yawancinsu 'yan kabilar Hutu ne. Wata mace mai shekaru 45 ta bayyana wa Amnesty International yadda wasu maza biyar suka yi mata fyade a sansanin 'yan tawayen M23 a watan Maris na wannan shekara ta 2025 a Boukavou, uku daga cikinsu na magana ne da harshen mutanen Ruwanda biyu kuma na magana da Harshen Suwahili. Dakarun M23 da gwamnatin Rwanda sun musanta zarge-zargen, amma Amnesty International da Human Rights Watch na kira ga Majalisar Dinkin Duniya da kasashen duniya su dauki mataki domin tabbatar da hukunta masu laifi. Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce, tashin hankali ya karu duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.