Zirin Gaza: Ko za a daina zubar da jini?
July 14, 2025Kakakin Hukumar Tsaron Fararen Hula ta yankin Zirin Gaza na Falasdinun Mahmud Bassal ya shaidawa kamfanin dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, Falasdinawa 10 ne aka kashe a sassa dabam-dabam na Zirin Gaza yayin hare-haren na Isra'ila a arewaci yayin da wasu 12 suka halaka a kudancin yankin Khan Yunis. Koda kamfanin dillancin labaran na AFP ya tuntubi rundunar sojojin Isra'ilan, sun shaida masa cewa suna gudanar da bincike kan rahoton.
Hare-haren na Isra'ila na zuwa ne, a daidai lokacin da rahotanni ke nuni da cewa masu rike da makamai na Falasdinun da sojojin Isra'ila na tunkarar juna a arewacin yankin Zirin na Gaza. Fito na fito na baya-bayan nan na zuwa ne, biyo bayan gaza cimma matsaya kan yaarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila da kungiyar Hamas mai gwawgarmaya da makamai a Falasdinun suka yi a tattaunawar da ba ta kai-tsaye ba da suke yi a Qatar.