Isra'ilawan da Hamas ta rike sun shaki iskar 'yanci
February 8, 2025Kungiyar Hamas mai iko daZirin Gaza, ta saki Isra'ilawa uku daga cikin wadanda take garkuwa da su a wannan Asabar, a yayin da ita kuma Isra'ilar ta sallamo Falasdinawa 183 da ta kama ciki har da wasu masu fada aji a kungiyar Hamas.
Wannan dai wani mataki ne na mutunta zango na biyar na yarjejeniyar tsagita buda wutarda bangarorin biyu suka cimma a Gaza, da shigar da kayayakin agaji, bayan da aka shafe watanni 16 ana gwabza fada.
Sojoji takwas da Hamas ta sako sun isa gida Isra'ila
Da sanyin safiyar yau ne Hamas ta mika mutanen uku da suka hada da Or Levy dan shekaru 34 da Eli Sharabi mai shekaru 52 sai kuma wani dan Isra'ila mai tsatso da Jamus Ohad Ben Ami mai shekaru 56 ga kungiyar agaji ta Red Cross.
A nata bangaren kungiyar agaji ta yankinZirin Gaza ta ce 7 daga cikin Falasdinawan da Isra'ila ta sako na bukatar kulawar gaggawa ta likita, kuma tuni aka garzaya da su a babban asibiti.
'Yan Isra'ila uku da Hamas ta sako sun isa gida
Ya zuwa yanzu daga cikin Isra'ilawa 251 da Hamas ta yi garkuwa da su wasu fiye da 70 na ci gaba da kasancewa a hannunta, a yayin da akalla 34 daga ciki suka rigamu gidan gaskiya a cewar ma'aikatar tsaron Isra'ila.