Yarima Harry na Burtaniya ya koka da janye jami'an tsaronsa
April 8, 2025Yarima Harry na Burtaniya ya bayyana gaban kotun masarautar kasar da ke birnin London, domin kalubalantar matakin gwamnati na janye masa jami'an tsaron lafiyarsa, bayan ajiye matsayinsa na 'dan gidan sarauta.
Karin bayani:Yarima Harry da mai dakinsa Meghan sun kammala ziyara a Najeriya
A shekarar 2024 ne babbar kotun London ta yanke hukuncin cewa matakin gwamnatin daidai ne, sannan ta haramta wa Yarima Harry daukaka kara, to daga bisani kotun daukaka kara ta sake sauraron korafinsa, bayan da lauyoyinsa suka nemi hakan.
Karin bayani:Yarima Harry a kotu kan rashin tsaro
Lauyarsa Shaheed Fatima ta bayyana wa kotun cewa hukumomin da alhakin kare 'yan sarauta da masu ruwa da tsaki na Burtaniya ya rataya a wuyansu sun nuna wa Yarima Harry wariya a cikin aikinsu, kuma hakan ba adalci ba ne.