'Yar majalisar dattawa a Najeriya ta tsallake kiranye
March 26, 2025Sama da mutane 250,000 ne dai aka ce sun mika wani korafi ga hukumar zaben tarayyar Najeriyar ta INEC. Korafin kuma da a cikinsa suke bukatar kiranye ga yar majalisar dattawa ta kasar Natasha Akpoti Uduaghan da ke tsakiyar wani rikici a zauren majalisar. To sai dai kuma wata sanarwa ta hukumar zaben dai ta ce masu korafin da ke zaman sama da kaso 50 cikin dari na masu zabe na mazabar Kogi ta tsakiyar basu cika ka'idar kiranye a kasar ba.
Karin Bayani:Cin zarafin jama'a ya karu a Najeriya
INEC din dai tace babu adireshi na daukacin mutanen dake bukata ta Kiranyen ko lambobi na wayarsu kamar yadda ka'idar kiranyen ta shekara ta 2024 ta tanadar. Duk da cewar dai an dade ana dakatar da yan majalisar dattawan bisa laifuka daban daban, wannan ne karo na farkon fari da ake shirin a janye wani dan dokar bisa laifi cikin gidan zauren dokar.
Rikicin na Natasha da majalisar dattawa ta kasar ta dakatar dai na neman bazuwa cikin kasar tsakanin wani kwamitin majalisar dattawa da kungiyoyin mata na kasar. Natasha Akpoti Uduaghan da ke wakiltar Kogi ta tsakiya dai na zaman daya a cikin mata guda hudu da ke zauren majalisar mai wakilai 109.
Kuma sata gaban a tunanin Hajiya Inna Chiroma da ke zaman tsohuwar ministan mata ta kasar kuma 'yar gwagwarmaya ta kare matan na zaman wani kokari na rushe siyasar mata a kasar. Duk da cewar dai matan suna kusan kankankan a cikin tarayyar Najeriya, kasa da kaso 10 cikin dari na mata na kasar ne dai ke taka rawa cikin batu na siyasar Najeriya.