'Yansandan Jamus na farautar wani mahari
May 19, 2025Talla
'Yansanda a Jamus, na farautar wani da ake zargi da kai hari da wuka a wata mashaya da ke birnin Bielefeld, inda ya jikkata mutane biyar a ranar Lahadi.
Hukumomin dai sun ce yanayin mutane hudu daga cikin su, wadanda suka jikkatarsu ta yi tsanani, inda guda ke cikin halin rai kokoi mutu kokoi.
Wadanda aka jikkatan matasa ne da ke tsakanin shekaru 22 zuwa 27 da haihuwa wadanda ke murnar nasarar kungiyar kwallon kafar yankin na Beilefeld a wata karawa da aka yi a karshen mako.
A cewar 'yansandan jihar North-Rhine Westphalia, mutumin da ake zargin ya arce daga inda ya aikata aika-aikar, kuma yana dauke da makami.
'Yansandan sun kuma fito hoton mutumin da ake zargi, wanda dan asalin kasar Siriya ne da ke da shekaru 35.