'Yan tawayen Mali sun saki direbobin Morocco da suka kama
August 5, 2025'Yan tawayen Mali masu alaka da kungiyar ta'addanci ta IS sun saki direbobin nan 4 'yan kasar Morocco da suka yi garkuwa da su tun cikin watan Janairun 2025, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tabbatar.
Kafar yada labaran Mali ta nuna hotunan direbobin 4 tare da shugaban gwamnatin mulkin sojin kasar Assimi Goita, a wani rahoto da ta yada cikin daren Litinin, wanda ta ce mutanen sun shaki iskar 'yanci ranar Lahadi.
Karin bayani:Mali ta soke yarjejeniya da 'yan tawayen Abzinawa
Tun farko 'yan tawayen sun kama direbobin tare da manyan motocinsu 3 na dakon kaya a cikin watan Janairun 2025, lokacin da suke kan hanyar Dori da ke Burkina Faso zuwa Tera a Jamhuriyar Nijar.
Karin bayani:'Yan tawayen Mali sun kashe gomman mayakan Wagner
Kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar, wadanda yanzu haka ke hannun sojoji, sun jima suna fama da hare-haren 'yan bindiga da kungiyoyin 'yan tawaye masu alaka da 'yan ta'adda a duniya irin su IS da Al-Qaeda.