SiyasaAfirka
Yan ta'addan IS sun halaka manoma 15 a Arewacin Najeriya
August 1, 2025Talla
Wasu daga cikin kungiyoyin da ke adawa da ayyukan ta'addanci a Najeriya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa 'yan ta'addan akan babura sun bude wuta kan mai uwa da wabi a kauyen Gurnowa dake da nisan kilomita biyar daga yankin Monguno.
Karin bayani: Harin kunar bakin wake ya halaka akalla mutum 12 a Borno
Guda daga cikin shaidun gani da ido Babagana Kolo, ya kuma shaida wa AFP cewa sun kwashe gawarwakin mutane 11 nan take a kan titunan kauyen, kuma sauran jami'an sa-kai da ke aiki da sojojin Najeriya sun je yankin domin dauko gawar wata mata da 'yayanta uku da suka mutu sakamakon taka nakiyar da aka binne a yankin na Monguno.