Nijar na alhinin mutuwar sojojinta 12 a fagen daga
April 27, 2025Ma'aikatar tsaron Nijar ta sanar da mutuwar sojoji 12 a yankin Tillaberi na yammacin kasar mai iyaka da Mali da Burkina Faso, yankin da ke zama tungar masu ikirarin jihadi da 'yan ina da kisa masu nasaba da 'yan kungiyoyin al Qaeda da IS.
Nijar: Zaman makoki bayan harin ta'addanci
Gwamnatin Nijar ta sanar da cewa an yi wa dakarunta na bataliyar ko-takwana mai suna Almahao kwanton bauna ne a wani kauye da ke kusa da Sakoira na yammacin Tillaberi, inda sojan suka jima suna barin wuta da 'yan ta'adda kafin a kawo musu dauki.
A baya gwamnatin kasar ta sanar da kashe 'yan ta'adda tara, ta kuma kwace makamai daga hannu masu ikrarin jihadi da suka kai wani harin da ta dakile a yankin.
Lakurawa na zafafa hare-hare a Jamhuriyar Nijar
A yankin Tahoua mai iyaka da Najeriya, rundunar tsaron Nijar din ta sanar da dauki ba dadi da Lakurawa masu yawan yin kutse kuma suna kai hari ga bututun man fetur dinta da ke zuwa gabar teku a Benin.
Rikicin yankin Sahel da ya samo asali daga kasar Mali a 2012, wanda kuma ya fadada har zuwa kasashen Burkina Faso da Nijar da kuma Benin ya halaka dubban mutane kama daga sojoji har zuwa farar hula.