'Yan ta'adda sun kashe sojojin Najeriya a Yobe
May 4, 2025Talla
Harin wanda majiyoyi daga soji suka tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP faruwar sa, ya kuma yi jallin bacewar wasu sojojin da dama.
'Yanbindigar dai sun afka wa sojojin ne a garin Buni Gari a daren Juma'ar da gabata, inda ma ta kai ga konewar sansanin sojojin bayan barin wuta.
Maharan dai sun kwashe makamai a barikin, kafin su cinna masa wuta.
Majiyoyin tsaron sun ce motoci da gine-gine da dama sun kone, amma kuma ba su bayar da adadi ba.
Barikin na Buni Gari dai shi ne na takwas da mayaka masu ikirarin jihadi ke kai wa hari cikin tsukin watanni biyu da suka gabata a Najeriyar.