SiyasaAfirka
Yan sandan Kenya sun cafke daruruwan masu zanga-zanga
July 1, 2025Talla
An dai tsara gudanar da zanga-zangar ce domin cika shekara guda da boren da al'ummar kasar su ka yi kan sabbin dokokin haraji da gwamnatin William Ruto ta bujiro da shi, wanda kuma ya rikide zuwa tarzoma sakamakon arangama da matasa suka yi da 'yan sanda.
Karin bayani:'Yan sandan Kenya sun tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga
Hukumar Kare Hakkin bil Adama ta Kenya ta sanar da cewa mutane 19 sun mutu, yayinda wasu kimanin 531 suka samu raunuka. Shugaban Sashen Binciken Manyan Laifuka na kasar Mohamed Amin, ya ce gwamnati ta cafke mutane 485, kuma ana zarginsu da aikata laifuka daban-daban ciki har da fasa shaguna baya ga kisa da kuma cin zarafi har ma da mallakar bingigogi ba bisa ka'ida ba.