Hukumomin Girka sun kama masu safarar mutane a Turai
May 22, 2025Talla
Rahotanni na nuni da cewar, an bai wa daruruwan bakin hauren jabun takardun tafiye-tafiye da ke ba da izinin tafiya zuwa wasu kasashe a cikin Tarayyar Turai.
Majiyar 'yansanda a Athens ta ce kungiyar ta samu kusan Euro miliyan 4 kwatankwacin dala miliyan 4.5 daga ayyukanta. Shugaban kungiyar, wanda aka ruwaito sauran mambobinsa na daga Siriya da Masar, na daga cikin wadanda aka kama, a cewar rahoton.
Jami’an ‘yan sanda na musamman sun kai samame a wasu wuraren da ke yankin Greater Athens, wanda kuma ya ke zama cibiyar ba da jabun takardu na tafiye-tafiye. An kuma kama wasu fasfo na jabu, tare da wasu ambaru.