'Yan sanda a Rasha sun kame masu zanga zanga
March 6, 2012Talla
Mutane kusan dubu 20 aka ƙiesta cewar sun gudanar da gangami na nuna adawa da nasarar da mista Vladmir Poutine ya samu da kusan kashi 64 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen wanda suka ce an yi maguɗi.
To sai dai wasu rahotanin na cewar an yi beli wasu shugabannin yan adawar guda biyu da aka tsare wato Alexei Navalny dakuma Sergeuei Oudalsov waɗanda za su iya fuskantar tarra har ta kuɗin Rasha Rouble dubu biyu ko wanne dangane da shirya gangami ba kan ƙaida ba.Yanzu haka dai sabon shugaban na Rasha na ci gaba da samun sakon taya murna daga shugabanin kasashen duniya waɗanda suka haɗa da na Jamus da Faransa da kuma Amurka.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou