Ana fama da karancin man fetur a Jamhuriyar Nijar
March 7, 2025Wannan dai shi ne karo na farko tun bayan da gwamnatin mulkin sojan Nijar ta rage kudin mai a bisa kiraye-kirayen talakawa 'yan Nijar musamman mazauna birnin Yamai da suka tsinci kansu cikin wannan hali na kanrancin man fetur. Malam Bio Abdourahmane wani dan fafutika kuma kwararre a harkar kasuwancin man fetur a Nijar ya bayyana wasu daga cikin dalilan da suka haifar da wannan matsala
"Matatar mai ta Damagaram tun ainihi an gina ta ne da nufin tace gangar mai dubu 20 a kowace rana da tunanin zai wadatar da kasa. Kuma a farko ya wadatar da kasar domin a lokacin da aka kafa ta, man Najeriya ana sayar da shi da arha. Shi ya sa 'yan Nijar da dama masamman mazauna kan iyaka babu ruwansu da man da ake haka a kasarsu domin suna samun na Najeriya. To man smogal na Najeriya da ake amfani da shi, sai ya hana a fahimci cewa man da matatar Damagaram ke samarwa ba ya isar kasar. Amma dai yanzu Najeriya ta dauke tallafin manta kuma man ya yi tsada, sai 'yan Nijar suka koma shan mai na kasa. Lokacin ne aka lura cewa matatar man ba ta iya biyan bukatar ‘yan kasa"
Sai dai Malam Mahamadou Gamatche shugaban hadaddiyar kungiyar dirobobin motoci a Nijar ya ce watanni da dama ke nan Nijar ke sayo mai daga waje duk da mallakarsa a cikin gida.
"Kamfanin SONIDEP watanni da dama kenan sai ya je kasashen waje ya yi odar mai saboda bukatar cikin gida, ana shigo da man daga Najeriya ko kuma daga Togo ta hanyar Burkina Faso. To amma saboda matsalar tsaro akan dauki loakci kamar watanni biyu zuwa uku kafin motocin su iso. Don haka muke bayar da shawarar a dunga tayar da tawaga ta musamman ta sojoji domin yin rakiyar motocin man tun daga tashar ruwa ta Cotonou har zuwa Yamai, sannan a gaggauta gina sabuwar matatar mai ta Dosso"
Wannan matsala ta karancin mai a Nijar na zuwa ne watanni kalilan bayan da kasar ta ninka danyen man da ta ke fitar wa zuwa gida wato ganga dubu 110 a rana da take sayar wa a kasuwar duniya ta hanyar tashar ruwan Cotonon kasar Benin. To sai dai wasu 'yan Nijar na danganta wanann matsala ta karancin mai da wasu matakai da gamwantin mulkin sojan Nijar din ta dauka. Malam Tchanga Tchalimbo na daga cikin masu irin wanann ra'ayi.
"Laifi kowa ya san na wadannan sojojin ne da suke kwashe manmu suna bai wa Mali da Burkina Faso. Kusan kyauta ne ake ba su. Ga arziki a kasarmu amma ba ya amfanar mu. Kuma abin takaici sun ki su sasanta da Benin a samu a bude iyaka a dunga shigo da man ta nan wajen balle a samu saukin lamurra"
Kawo yanzu dai kamfanin dillanci mai na kasa SONIDEP da Matatar mai ta Soraz da ma kungiyar masu motocin dakon mai kowane na nisanta kansa da kasancewa ummulhaba'isin wannan matsala. Wannan ta sanya 'yan kasa suka fara kiraye-kirayen ganin gwamnatin ta fito fili ta yi wa 'yan kasa bayani kan takamaiman abin da ke faruwa a wannan matsala ta karancin mai a Nijar: