Yan kasuwar arewa sun dakatar da kai kaya kudu
December 16, 2022A yayin da aka shiga rana ta biyu ta wani yajin aikin dillalai na abincin da suka toshe hanyoyin zuwa kudancin tarrayar Najeriya, yajin daga dukkan alamu na shirin barin baya da kura in da kungiyar dillalan kasar ta ce, ba da yawunta ake yi ba. Batun na abinci dai daga dukkan alamu na neman zama sabo na makami cikin bakar siyasar da ke ta yaduwa a tarrayar Najeriya a halin yanzu.
Kuma an shiga rana ta biyu tare da wani yajin aiki a bangare na wata kungiyar masu kaasuwar ta arewa da ke fadin tura ta kai bango kuma an kare musu hakuri. Yawan kisa na masu kasuwar a sashe na kudu maso gabashin tarrayar Najeriyar, na zaman hujja ta masu kasuwar ta arewa da ke fadin sun tsayar da kai kaya zuwa kudanci na kasar.
To sai dai kuma wani gamin gambiza na kungiyoyin dillalai na abincin, sun ce babu yawunsu cikin yajin aikin da a fadar shugaba na kungiyar comrade Muhammad Taheer ke iya kai wa ga asara ta a kokari na gyara ga gira. Koma ya take shirin da ta kaya a tsakanin ma su barazanar jefa kudancin kasar a cikin halin yunwa, da kuma masu tunanin asarar na ga masu kasuwar ta arewa dai, daga dukkan alamu sabon rikicin na dada tasiri ga tattali na arzikin tarrayar Najeriya a halin yanzu ba.
Ya zuwa wannan Juma'a, babban titin da ya hade sashen arewacin kasar da kudancinsa na cushe a garin Abaji da ke iyakar babban birnin tarraya Abuja da jihar kogi, sakamakon toshe hanyar da kuma tsayar da daukar kaya a tsakanin sassan tarrayar Najeriyar guda biyu. Duk da cewa, zai dauki lokaci kafin a iya tantance irin girma na asara da kila ma tasirinta ga tattali na arzikin Najeriyar, akwai dai tsoron rikicin na iya kara jefa al'ummar da ke shirin biki da hutu na shekarar cikin wani yanayi maras dadi.