SiyasaAfirka
An yi garkuwa 'yan China uku a kasar Ghana
March 31, 2025Talla
Ma'aikatar Harkokin Wajen China ta bayyana cewa al'ummar kasarta guda uku da aka yi garkuwa da su a kasar Ghana na nan cikin koshin lafiya, duk da cewa bata bada cikakken bayani kan halin da suke ciki ba.
Karin bayani:An sace 'yan Koriya ta Kudu uku a gabar kogin Ghana
A nata bangaren gwamnatin Ghana ta kaddamar da bincike kan batan dabon da wasu 'yan China uku suka yi a lokacin da aka kai wa jirgin ruwansu hari a tsakiyar gabar tekun Guinea.