'Yan Houthi sun yi barazana ga Amurka
June 21, 2025'Yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun yi barazanar kai wa jiragen ruwan Amurka hare-hare a Tekun Bahar Rum, idan har Washington ta yi kuskuren shiga yakin da Isra'ila ta kaddamarwa Iran, duk kuwa da yarjejeniya tsagaita wuta da aka cimma a baya-bayan nan.
A cikin wani faifan bidiyo kakakin 'yan tawayen Houthi Yahya Saree ya bayyana cewa muddin Amurka ta kai wa Iran hari ko kuma ta shiga cikin wannan rikici, mayankansu za su kaddamar da farmaki kan muradun Amurkar da suka hada da jiragen yaki da kuma jiragen dakon kaya da ke zirga-zirga a Tekun Bahar Rum.
Wannan barazana ta 'yan tawayen Houthi na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donad Trump ya saka wa'adin makonni biyu domin yanke shawara a game da yiwuwar shiga rikicin da ya barke tsakanin Isra'ila da Iran inda aka shiga mako na biyu suna yi wa juna ruwan bama-bamai.