Harin Isra'ila ya halaka firaminista a Yemen
August 31, 2025Talla
Wani harin jirgin yakin Isra'ila ya kashe Firaministan gwamnatin da 'yan tawaye ke jagoranta a Sanaa babban birnin Yemen, a cewar mayakan Houthi da ke samun goyon bayan Iran.
Ahmed Ghaleb Nasser Al-Rahawi da wasu ministoci ne dai aka kai hari a kansu a Yemen din.
Tuni ma aka nada Mohammed Ahmed Miftah, mataimakin firaminista, a matsayin firaminista na rikon kwarya.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai harin ne a kan wata muhimmiyar cibiyar mayakan Houthi.
Al-Rahawi dai ya rike mukamin firaminista ne tun daga Agustan bara.
Akalla mutane 10 sun mutu yayin harin, wasu 102 kuma suka samu raunuka, in ji ma'aikatar lafiya da gwamnatin ‘yan Houthi.