SiyasaAfirka
Yan bindiga sun kashe manoma tara a Jangebe na jihar Zamfara
July 19, 2025Talla
Wasu mazauna yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa baya ga mutanen da suka halaka sun kuma yi garkuwa da wasu karin mutanen akalla 15. Kazalika shugaban karamar hukumar Talata Mafara Yahaya Yari Abubakar, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce shi da kan sa ya jagoranci yi wa mamatan sutura.
Karin bayani:A Najeriya 'yan bindiga sun tashi kauyuka da dama
Gwamnatin jihar Zamfara ta dauki hayar 'yan banga da sauran kungiyoyin sa-kai wajen taimaka mata a yaki da 'yan bindigar daji. Ko a watan Yunin 2025, gamayyar jami'an tsaro a jihar sun yi nasarar kashe 'yan ta'adda akalla 100 a dazukan da ke karamar hukumar Shinkafi.