'Yan bindiga sun kashe kusan mutum 20 a jihar Naija
July 10, 2025
Talla
'Yan ta'addan daji sun kashe mutane 17 cikinsu har da jami'in dan sanda daya, a wani mumunan hari da suka kai a kauyen Mangwaro da ke karamar hukumar Mariga a jihar Naija da ke Arewa maso Tsakiyar Najeriya.
Bayanai sun tabbatar da cewa karamar hukumar Mariga na fusknatar karin masu kai hare-hare, wadanda tserewa daga jihohin Zamfara da Kebbi inda ake far masu da hare-hare babu kakautawa.
Harin ya jefa al'umma cikin fargaba kamar yadda shugaban karamar hukumar Mariga, Alhaji Abbas Kasuwar Garba ya bayyana.
Ko a watan jiya sojoji 17 suka rasa rayukansu, lokacin da 'yan bin digar sama da 100 suka afkawa wani sansanin sojoji da ke a kauyen Bangi, a jihar ta Naija