'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro 13 a Zamfara
August 10, 2025Wasu 'yan bindiga sun halaka jami'an tsaro 13, ciki har da ‘yan sanda biyu da ‘yan sa-kai 11, a jihar Zamfara da ke Arewa maso yammacin Najeriya.
Wannan harin wani sabon tashin hankali ne a yankin, kamar yadda mazauna suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Lahadi.
An sace sama da mutane 60 a Zamfara
'Yan bindiga sun dade suna addabar al'ummomi a arewa maso yamma da tsakiyar Najeriya, sannan suna kai hare-hare kan kauyuka da sace mutane da kona gidaje.
A cewar majiyoyin, ‘yan bindigan masu yawan gaske sun mamaye kauyen Adabka da ke Bukkuyum a daren Juma'a, sannan suka sace wasu mazauna kauyen tare da tserewa da su zuwa cikin daji.
Najeriya: 'Yan bindiga sun kashe mutane 33 a jihar Zamfara
Har ila yau, sun yi kwanton bauna suka bude wuta kan tawagar ‘yansanda da ‘yan sa-kai da ke bin su domin ceto wadanda aka sace.