'Yan aware sun halaka mutane 20 a Kamaru
November 6, 2023A cewar mahukutan yankin wannan lamari ya auku ne a daren Lahadi wayewar Litinin a wani kauyen da ake kira Egbekaw wanda ke yankin Kudu maso Yammacin kasar inda baya ga mutuwar mutane 20 suka tabbatar da jikkatar karin wadansu mutane 10.
Karin bayani: 'Yan awaren Kamaru sun yi garkuwa da mata
Wata majiya daga jami'an tsaron kasar ta ce 'yan awaren sun kona gidaje da dama a yayin harin sannan kuma ana ci gaba da kara tantace adadin wadanda lamarin ya ritsa da su wanda ka iya karuwa nan zuwa gada.
Karin bayani: 'Yan aware sun yi kashe-kashe a Kamaru
Tun a shekarar 2016 ne dai ake fama da kazamin tashin hankili da ke lakume rayukan jama'a a yankunan Arewa maso Gabashi da kuma Kudu masu Yammacin Kamaru inda kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa ke zargin sojojin gwamnati da 'yan aware da aikata laifukan yaki.