Ina makomar 'yancin kan Yammacin Sahara?
June 11, 2025Birtaniya ta sake karfafa matsayi kan rikicin yankin Yammacin Sahara, ta hanyar goyon bayan shirin kasar Maroko na kwarya-kwaryar 'yanci. Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy ne ya bayyana matsayin lokacin ziyararsa a kasar Morokon a farkon wannan wata, inda ya ce matakin na Maroko ya nuna sanin ya kamata. Kafin wannan lokaci Birtaniya tana goyon bayan burin Majalisar Dinkin Duniya, kan warware rikicin na Yammacin Sahara.
A shekara ta 2007, Maroko ta gabatar da wani shiri na kwarya-kwaryar 'yanci ga Yammacin Sahara karkashin ikon kasar. Isabelle Werenfels masaniyar kasashen yankin Maghreb da ke Cibiyar Nazarin Harkokin Kasashen Ketere da Tsaro a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus, na ganin kasashe da dama suna matsawa zuwa bangaren Maroko.
Yankin Yammacin Sahara ya kasance karkashin ikon Spaniya a karni na 20, amma zuwa shekara ta 1976 lokacin da ta fara janyewa sai Maroko wacce dama ta mamaye arewacin yankin ta yi amfani da damar wajen mamaye kudancin yankin. Ita kuwa Aljeriya na goyon bayan 'yancin Yammacin Sahara, kuma an gwabza yaki har zuwa tsagaita wuta a shekara ta 1991. Hasni Abidi masanin harkokin siyasa daga kasar Aljeriya, na ganin goyon bayan manyan kasashe ga Maroko a matsayin juya baya ga Aljeriya.
Kasashen Maroko da Aljeriya suna zaman doya da man ja a kan batun na Yammacin Sahara, inda Aljeriya take goyon bayan 'yan Polisario kan gwagwarmayar 'yanci. Maroko kuma na da hulda ta kut da kut da manyan kasashen da ke cikin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, amma ba haka batun yake ba ga Aljeriya.