SiyasaJamus
Yaki: Jamus za ta rufe ofishin jakadancinta a Sudan ta Kudu
March 22, 2025Talla
Jamus ta sanar a wannan Asabar cewa za ta rufe ofishin jakadancinta na birnin Juba a kasar Sudan ta Kudu, sakamakon fargabar sake barkewar yakin basasa.
Karin bayani:Sharhin Jaridun Jamus a kan nahiyar Afirka
Ministar harkokin waje Annalena Baerbock ta zargi shugaban kasar Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar da ingiza zaman tankiyar da ke shirin jefa kasar cikin yaki, bayan shekaru ana samun kwan-gaba-kwan-baya a fannin tsaro, kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.
Karin bayani:Cafke ministan man fetur a Sudan ta Kudu
A ranar Talata manyan kasashen duniya suka nemi shiga tsakani wadanda suka hada da Canada da Jamus da Netherlands da Norway, sai Burtaniya da Amurka da kuma kungiyar tarayyar Turai EU don samun wanzuwar zaman lafiya a kasar.